Sakataren Wajen Burtaniya yana ziyara a Burma

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption William Hague

Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya, William Hague, ya ce shugabannin Burma sun ba shi tabbacin cewa za su saki daukacin fursunonin siyasa, kuma ba za su fasa sauye-sauyen da suke aiwatarwa a kasar ba.

Sauye-sauyen da aka samu na baya-bayan nan, ciki har da matakan halalta kungiyoyin kwadago, da cire takunkumin da aka kakabawa kafafen yada labarai da kuma sakin wasu fursunonin siyasa, su ne suka karfafa gwiwar jami'an diflomasiyyar Yammacin duniya.

Ana sa ran Mista Hague, wanda ke wata ziyara ta kwanaki biyu a kasar ta Burma, zai gana da Shugaba Thein Sein da kuma jagorar 'yan rajin dimokuradiyya, Aung San Suu Kyi, da ma jagororin kananan kabilun kasar.

Ana kuma sa ran Mista Hague zai kara matsin-lamba a kan gwamnatin Burma ta ci gaba da shirinta na sakin fursunonin siyasa ta kuma shirya zabuka na gaskiya da adalci a watan Afrilu.

Wannan ce dai ziyara irinta ta farko a cikin fiye da shekaru hamsin.

Karin bayani