Ana shirin sanyawa Iran takunkumi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Iran Mohammed Ahmedinejad

Ministan Harkokin Wajen Faransa, Alain Juppe, ya ce Tarayyar Turai na gab da kakabawa Iran takunkumin hana ta fitar da man fetur zuwa kasashen waje.

Mista Juppe ya ce, ''Muna da taron ministocin harkokin waje ranar 30 ga watan Janairu, ina kuma fatan a lokacin ne za mu yanke shawara a kan kakabawa Iran takunkumin hana sayar da man fetur din nata a kasashen waje''.

Iran dai na samun rabin kudaden shigarta ne daga man fetur din da take fitarwa; takunkumin kuma zai tilasta mata garzawa nahiyar Asiya don neman cike gibin cinikayyar da zai biyo baya.

Gwamnatin Amurka ta yi marhabin da matakin, tana cewa Tarayyar Turai ta yi daidai da ta kai wannan gaba.

A yanzu dai, kasashen Tarayyar Turan na sayen kashi 17 cikin dari na man da Iran ke samarwa.

Sai dai ko da kasashen Tarayyar Turan sun amince da wannan mataki, za a iya daukar watanni da dama ba tare da an aiwatar da shi ba.

Hakan dai na zuwa ne bayan da Amurka ta sanyawa wata doka hannu, wacce ke neman hukunta duk wani kamfanin kasashen waje da ya sayi man Iran.