An bukaci hukuncin kisa ga Mubarak

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hosni Mubarak

Hosni Mubarak: Masu shigar da kara a Masar sun bukaci hukuncin kisa

Masu shigar da kara a shari'ar tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak sun bukaci a yanke masa hukuncin kisa.

Mr Mubarak na fuskantar shari'a a birnin Alqahira bisa zargin bada umurni kashe masu zanga zanga a lokacin da aka yi boren da ya sa aka hambarar da gwamnatinsa a watan favraru na shekerar data gabata.

'Yayan Mr Mubarak su biyu, Gamal wanda a baya shine aka rika tunanin zai gaji mahaifinsa da kuma Alaa na fuskantar zargin aikata rashawa a shari'ar.

"Ya za'a yi a ce shugaban jamhuriya be san da zanga zangar da aka gudanar a ranar ashirin ga watan janairu" tambayar da Mr Suleiman yayi kenan.

Mr Suleiman ya ce ministan cikin gida na wancan lokaci, Habib EL-Adly , wanda shima ana tuhumarsa a shari'ar, ba zai iya bada umurni a harbi masu zanga zanga ba, ba tare da Mr Mubarak ya bashi umurnin yin haka ba."