Mutane ashirin da shida sun halaka a Congo

genocide Hakkin mallakar hoto Sygma
Image caption Kusan akala mutane miliyan daya ne aka kashe a Rwanda

Rundunar sojin jamhuriyar demokradiyar Congo tace akala mutane ashirin da shidda suka halaka a hare haren da mayakan sa kai na kasar Rwanda suka kai a gabashin kasar.

Tace kauyuka da dama a yankin kudancin Kivu an rika kai musu hari tun farkon watan janairu na shekerar da muke ciki.

Wani kakakin Sojin kasar ya dora alhaki akan dakarun kungiyar FDLR dake fafitukar kwato Rwanda wadda ta saba kaiwa farar hular yan kasar Congo hari.

Yace rundunar soji ta aike da karin sojoji zuwa yankin, sai dai wadanda aka kashe dukaninsu farar hula ne a cewar kakakin sojin Congo Sylvain Ekenge.

Yace wasu gungun mayakan sa kai sun kai hari a wasu matsugunai kuma sun kona gidaje a yankin Shabunda wani daji a kudancin Kivu a ranar biyu da uku ga watan janairu.

Mazauna kauyen sunce an kaimusu harin ne saboda suna goyon bayan wata kungiya na mayakan sa kai a cewar kwanel Ekenge.

Sai dai yace tuni sojoji suka dauki matakin neman mayakan da suka aikata wanan aika aika.

Harin Kigali

Tashin hankalin na daya daga cikin tashe tashen hankula mafi muni da kungiyar FDLR zata kai a watani da dama da suka gabata.

A watan disemba kotun sauraren manyan laifuka ta duniya a Hague ta sako daya daga cikin shugabannin kungiyar, Callixte Mbarushima bayan alkalai sun yanke hukunci akancewa babu wani kwakwaran shaida bisa zargin da ake masa.

Ya musanta biyar daga cikin laifukan da ake zarginsa da aikatawa da suka hada da kisan kare dangi da takwas daga cikin zargin da ake masa na aikata laifukan yaki da suka hada da kisa, azabtarwa, fyade da kuma lalata dukiyoyi.

Kungiyar na daya daga cikin kungiyoyin sa kai masu rike da makamai masu tasiri a gabashin demokradiyar Congo fiye da shekaru takwas bayan an kamala yakin basasa a kasar

Ana zargin mayakan kungiyar FDLR da aiwatar da fyade da dama da kuma kashe kashe, duk da cewa akwai dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya a yankin.

Kabilar hutu ne suka kafa kungiyar ta FDLR wadanda suka tsere daga Rwanda wacce ke makwabtaka da Congo bayan kisan kare dangi da ya faru a shekerar 1994.

A wani labarin kuma mutane biyu suka halaka a wani harin da akayi amfani da girneti a Kigali babban birnin kasar Rwanda, yayinda goma sha shida sun samu raunuka.

Dakarun kasar son dora alhaki akan harin da akayi a baya makamanci haka akan kungiyar ta FDLR.

Karin bayani