'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Kano

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga a Najeriya

A Najeriya, 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga, wadanda suka yi zaman dirshan a tsakiyar birnin Kano, domin bijirewa matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na cire tallafin man fetur.

Masu zanga-zangar dai, wadanda suka kuduri aniyar kwana suna zaman dirshan din duk kuwa da hunturun da ake yi, sun ce sun samu kwarin gwiwa ne daga boren da aka yi a kasashen Larabawa - abin da ya sa suka yiwa sha-tale-talen da suka mamaye lakabi da Dandalin Tahrir. Sai dai sun yi zargin cewa 'yan sanda sun fatattake su, sannan suka kama mutane goma sha tara daga cikinsu, ko da yake daga bisani sun sallame su.

Wakilin BBC a Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai, ya yi kokarin jin dalilan da suka sanya rundunar 'yan sandan jihar ta kori masu zanga-zangar duk da yake basu yi yunkurin tayar da hankali ba, amma bai samu kakakin rundunar ta wayar salula ba.

Ba gudu-ba-ja-da-baya

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC a Najeriya sun yanke shawarar fara yajin aikin gama-gari a ranar Litinin mai zuwa don nuna rashin amincewa da cire tallafin.

Kungiyoyin kwadagon sun ce za su tafi yajin aikin sai baba ta gani. Shugabannin kungiyoyin kwadagon sun yanke hukuncin tafiya yajin aikin ne bayan wata ganawa da suka yi ranar Laraba.

Gwamnatin Najeriyar dai ta janye tallafin man ne a ranar Lahadin da ta gabata, abin da ya sa farashin mai a kan lita ya tashi daga naira 65 zuwa naira 144.

Miliyoyin 'yan Najeriya ne dai ke fama da matsanancin talauci, inda suke rayuwa a kasa da dalar Amurka daya a rana.

Tun lokacin da aka sanar da janye tallafin man a ranar Lahadi ake gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na Najeriyar - al'amarin da har ya kai ga asarar rayuka, yayin da wani mai fafutuka a Legas kuma ya fara yajin cin abinci domin matsawa gwamnatin lamba.

Karin bayani