'Yan kwana-kwana sun mutu a Chile

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wutar daji a Chile

Hukumomi a Chile sun ce 'yan kwana-kwana shida sun rasa rayukansu yayinda suke yunkurin kashe wutar da ta tashi a wani daji mai tsaunuka a kudancin kasar.

Wasu da dama kuma sun kone lokacin da iska ta kada ba zato ba tsammani, harshen wutar ya yi musu kawanya.

Shugaba Sebastian Pinera ya ce alamu na nuna cewa da gangan aka kunna wutar, ya kuma ce za a hukunta wadanda ke da alhakin kunnata:

''Mun yanke shawarar amfani da dokokin ta'addanci don hukunta wadanda suka kunna wutar, don ba ko tantama wannan mugun laifi ne saboda da gangan aka kunna wutar a wurare da dama a lokaci guda''.