An hallaka mutane shida a Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojoji na aiki a wani waje da aka kai hari a Najeriya

Wadansu 'yan bindiga sun hallaka akalla mutane shida a wani harin da aka kai kan wata majami'a da ke garin Gombe a arewa maso gabashin Najeriya.

Wani wanda ke asibitin garin lokacin da aka kai wadanda abin ya rutsa da su ya shaidawa BBC abin da ya gani:

''Na ga gawawwaki shida;guda hudu an kawo su a idanu na, akwai yaron da ya cika a asibiti, haka kuma akwai wata mace da ta mutu''.

Paston majami'ar ya ce an kai harin ne yayin da suke ibadar yamma; ya kuma kara da cewa maidakinsa na cikin wadanda suka rasa rayukansu.

Ya zuwa yanzu dai ba a san wadanda suka kai harin ba; amma kuma a 'yan makwannin da suka gabata kungiyar nan ta Boko Haram ta kai hare-hare, ta kuma ce tana so Kiristoci su bar yankin.

Gwamnati dai ta kafa dokar ta-baci a wasu sassa na arewacin Najeriyar.

Karin bayani