'Kaifin kwakwalwa na fara raguwa daga shekaru 45'

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Hoton kwakwalwar dan adam

Wani sabon bincike ya nuna cewa mantuwa na karuwa kuma karfin kwakwalwa na gudanar da wasu ayyuka na fara raguwa ne lokacin da mutum ya haura shekaru arba'in da biyar a duniya.

A wata kasida da suka wallafa a mujallar British Medical Journal, masana kimiyyar da suka gudanar da binciken sun ce sun yi nazari ne a kan kaifin kwakwalwar ma'aikatan gwamnati 7,000 a Burtaniya, wadanda shekarunsu suka kama daga arba'in da biyar zuwa saba'in a tsawon shekaru goma.

Abin da ya ba da mamaki shi ne cewa kaifin kwakwalwar mutanen da shekarunsu suka kama daga shekaru arba'in da biyar zuwa arba'in da tara ya ragu da kashi uku cikin dari.