Yajin aiki ya tsayar da al'amura cik a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AP

Yajin aikin gama-gari da kungiyoyin kwadago suka kira a Najeriya kan matakin gwamnati na janye tallafin man fetur ya tsayar da al'amura cik a kasar baki daya.

Shaguna da ofisoshin gwamnati da makarantu da gidajen man fetur da ma bankuna sun kasance a rufe a duka fadin kasar a ranar farko ta yajin aikin na sai baba-ta-gani.

Dubban jama'a ne suka yi maci a Legas da sauran biranen kasar domin nuna adawa da cire tallafin man.

An samu tashin hankali tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro, inda aka kashe mai zanga-zanga guda a Legas.

An kashe mutane

Wakilin BBC a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai yace akalla mutane 20 ne suka jikkata bayan da jami'an tsaro suka bude wuta kan masu zanga-zangar.

"Jami'an 'yan sanda sun ce mutum guda ya rasa ransa", amma majiyar asibiti ta tattabatarwa da BBC mutuwar mutane biyu, yayin da wakilinmu ya ce wasu mazauna birnin sun ce mutane hudu ne aka kashe a zanga-zangar.

Tuni mahukunta a jihar suka kafa dokar hana zirga-zirga daga karfe shida na yamma zuwa takwas na safe sakamakon tashin hankalin da aka samu a lokacin zanga-zangar.

Shugaba Goodluck Jonathan ya ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da daukar nauyin tallafin man ba.

A kalla mutane 10,000 ne suka shiga zanga-zangar a jihar Legas domin neman gwamnatin ta sauya matsayarta.

Yayin da a Kaduna ma wakilinmu Nura Muhammad Ringim ya ce dubban daruruwan mutane ne suka halarci zanga-zangar karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Alhaji Balarabe Musa da kuma dan rajin kare hakkin bil'adama Malam Shehu Sani da jami'an kungiyar kwadago.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun daga kwalayen da ke nuna adawa da gwamnatin Shugaba Goodluck.

ba su damu da halin da muke ciki ba

A Abuja babban birnin kasar, kungiyoyin kwadago sun gudanar da zanga-zanga inda suka hana zirga-zirgar jiragen sama.

"Shugabannin mu ba su damu da halin da muke ciki ba," kamar yadda wani mai zanga-zanga ya shaida wa BBC.

Farashin mai da na sufuri sun ninka tun ranar 1 ga watan Janairu loakcin da aka sanar da janye tallafin.

Yawancin 'yan kasar na ganin wannan ne kawai abinda suke amfana daga gwamnati.

Ministan sadarwa na kasar Labaran Maku ya yi kira ga 'yan kwadagon da su kawo karshen yajin aikin na su, yana mai cewa a shirye gwamnati ta ke a fara tattaunawa.

Ya shaida wa BBC cewa a shirye mahukunta suke su gudanar da ayyukan ci gaban kasa domin rage radadin janye tallafin.

Wani yajin aiki makamancin wannan a shekara ta 2003 ya kare da samu matsaya lokacin da gwamnati ta rage kudaden da take bayarwa maimakon janye su gaba daya.

Karin bayani