Jam'iyyar ANC ta Afrika ta Kudu ta cika shekaru 100

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jam'iyyar ANC me mulki a Afrika ta Kudu

Jam'iyyar ANC ta Afrika ta Kudu ta cika shekaru dari da kafuwa.

An fara bukukuwan cikar jam'iyyar shekaru dari ne da wasan Golf.

Mutane fiye da dubu dari daya ne ake sa ran zasu halara garin Bloemfontein a karshen makon nan.

Sauran bukukuwan da za'a gudanar sun hada da adu'oin da ake yi da kyandura a cikin wani coci inda a nan ne aka kafa jam'iyyar ta ANC, da kuma wani babban gangamin siyasa a ranar Lahadi .

An dai kafa jam'iyyar ta ANC ce domin ta yaki mulkin wariyar launin fata da ya zo karshe a shekerar 1994.

Ita ce jamiyya mai tsawon shekaru a Afrika da ta rika Fafutukar kwato yanci.

Nelson Mandela wanda ya jagoranci ANC ta mulki kasar bayan da aka kawo karshen mulkin wariyar launin fata ba zai halarci bukukuwan ba.

Tsohon shugaban kasar mai shekaru casain da uku da haihuwa, bai halarci wani taro ba tun shekarar da ta gabata.

Shugabar jam'iyyar ta ANC Baleka Mbete ta maida martani kan zargin da ake akan cewa wasan golf din da aka fara bukukuwan da shi wata alama ce ce akan yadda masu hanu da shuni ke cigaba da karuwa a jam'iyyar mai mulki.

"ANC jam'iyya ce da asalinta ta mazauna karkara ce kuma za ta ci gaba da kasancewa haka" In ji Mbete, a wata hira da ta yi da manema labarai a kasar.

Ta ce "Idan ka dubi bukukuwan da za'a gudanar a garin Bloefontein zaka ga komai an shirya shi ne domin mutanen da ke karkara. Dukanin membobinmu na can suna wa filin wasanni kwalliya kuma suna magana da mazauna karkara.

Andrew Mlangeni wanda ya shigo jam'iyyar a shekarar 1951 kuma ya shafe tsawon shekara a gidan yari dake tsibirin Robinson shi ne ya fara buga kwallon golf din.

Karin bayani