Gwamnatin Jihar Adamawa a Najeriya ta kafa dokar hana yawon Jama'a

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani waje da harin bam ya lalata a Najeriya

Gwamnatin Jihar Adamawa a Najeriya ta saka dokar hana fitar Jama'a a dukanin fadin Jihar.

Wannan ya biyo bayan hare haren da wasu yan bindiga suka kai a jihar Jiya inda suka harbe mutane fiye da 25 har lahira.

Sojoji da Yansanda suna ta zagaye, yayinda wasu kuma suka yiwa wuraren da aka kaiwa harin kawanya

Haka nan kuma an hana dukanin wasu harkoki na kasuwanci a garin Yola.

Wannan na daga cikin tsananta kai hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa a kan Cocic coci a yankin arewa maso gabacin kasar.

A kwanakin biyun da suka gabata akalla mutane ashirin ne suka rasa rayukansu a yankin.

Ko da a daren ranar Juma'a rahotanni daga Jihar Adamawa sun ce wasu 'yan bindiga wadanda ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan wata majami'a a Yola, babban birnin Jihar, sun kuma hallaka akalla mutane 11.

Hakan dai ya faru ne bayan wani harin da aka kai a garin Mubi da ke jihar ranar Juma'ar da rana, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane goma sha biyu.

Ya zuwa yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da harin na Yola ya shafa ba, kuma hukumomi ba su yi karin bayani ba.

An yi dauki-ba-dadi a Yobe

A garin Potiskum da ke jihar Yobe ma a yankin na arewa maso gabashin Najeriya, rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa an kwashe daren ranar Juma'a ana bata-kashi tsakanin 'yan sanda da 'yan kungiyar Boko Haram.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Lawal Tanko, ya shaidawa BBC cewa an samu asarar rayuka yayin taho-mugamar, sai dai ya ce ba zai yi karin bayani game da adadin mutanen da suka mutu ba kasancewar suna ci gaba da tattara bayanai.

Tun da fari dai, mazauna birnin sun shaidawa BBC cewa sun ji karar harbe-harbe da kuma fashewar wasu abubuwa, al'amarin da ya tayar musu da hankali.

A 'yan makwannin nan kungiyar ta Boko Haram ta kaddamar da hare-hare a kan Kiristoci a arewacin Najeriyar.

Karin bayani