Sojin Kenya sun yi ikirarin cewar Al Shabaab na samun koma baya

Sojojin Kenya a Somalia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Kenya a Somalia

Rundunar sojan Kenya ta ce an fara karya lagon kungiyar 'yan kishin Islama ta al-Shabaab a Somalia, yayinda hare haren da dakarun Kenya a cikin Somaliyar ke kara zafafa.

Kakakin sojan ya shaidawa manema labaru a Nairobi cewa samun rarrabuwar kawuna a tsakanin shugabanin kungiyar ta Al-Shabaab na nufin cewa karshenta ya kusa.

Ya ce, a jiya da misalin karfe uku na yamma sun kai hare hare ta sama a Garbahare.

Yawan wadanda hare haren suka shafa na da matukar dama.

Ya ce harin ya kashe mayakan al-Shabaab din akalla su sittin, kuma wasu ashirin sun sauya sheka a cikin makonni biyun da suka wuce.

Sai dai wakilin BBC a Gabashin Afrika na cewa abu ne mai matukar wuya a iya tantance wadannan rahotanni. Al-Shabaab ta ce zata murkushe dakarun Kenyar.

Karin bayani