Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci mayar da tallafin man fetur

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Goodluck Jonathan

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci a jingine matakin janye tallafin man petur.

A lokacin wani zaman gaggawa, kudirin majalisar ya nemi da a kara tattaunawa kan matakin da gwamnatin ta dauka, wanda ya sa farashin mai ya ninka.

Haka nan kuma majalisar ta bukaci kungiyar kwadago ta kasar da ta jingine aniyar yajin aikin da ta kudurci somawa a gobe,

Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonthan, ya kare matakin da ya dauka na janye tallafin man fetur, inda ya ce ya dauki matakin ne don inganta tattalin arzikin kasar.

Tun bayan sanarwar janye tallafin a makon da ya gabata dai, farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi.

A jawabinsa na mai da martani a hukumance na farko, shugaban kasar ya yi kira ga 'yan Najeriya su goya masa baya:

''Zan so in yi amfani da wannan dama in tabbatarwa 'yan Najeriya cewa ni ma fa ina jin irin radadin da dukkanku ke ji na hauhawar kudin mota da farashin kayayyakin masarufi''.

Shugaban kasar ya kuma ba da sanarwar rage albashin manyan ma'aikatan gwamnati da kashi ashirin da biyar cikin dari, da kuma soke tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, sai dai wadanda suka zama dole.

Sai dai kungiyoyin kwadagon kasar sun ce jawabin shugaban kasar bai gamsar da su ba, suna masu cewa babu-gudu-babu- ja-da- baya game da yajin aikin gama-gari da zanga-zangar da suka shirya farawa a ranar Litinin.