Akwai yan Boko Haram a cikin Gwamnati -- Inji Shugaba Goodluck

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya ya ce a yanzu kungiyar Boko Haram na da magoya baya,da ma mabiya a cikin gwamnati, da a rundunar sojoji da kuma a hukumomin tsaron kasar.

Mutane sama da tamanin ne aka kashe a 'yan makonnin da suka wuce, a hare haren da 'yan kungiyar suka rika kaiwa.

Shugaba Jonathan ya ce matsalar tsaron da aka shiga yanzu ta fi ta lokacin yakin basasar kasar na shekarun 1960 sarkakiya, inda aka kashe mutane sama da miliyan guda.

A jiya ne shugaban kungiyar Kiristocin Nijeriyar yayi gargadin cewa kasar na kusantar tsunduma cikin yakin basasa.

Karin bayani