Kungiyar kasashen Larabawa za ta ci gaba da aikin sa ido a Syria

Wani taron kungiyar kasashen Larabawa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani taron kungiyar kasashen Larabawa

Ministocin harkokin waje na kungiyar kasashen Larabawa dake taro a Alkahira sun ce tawagar sa idon da suka tura Syria za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta, duk da irin sukar da ake yi cewa ta gaza wajen dakatar da kisan da dakarun gwamnati ke yi wa fararen hula.

Wakilin BBC ya ce, Ministocin sun saurari cikakken bayani daga shugaban tawagar sa idon a Syria, tare da duba tasirori da hotuna na irin abubuwanda suka ganewa idanunsu.

'Yan adawar Syria sun yi kakkausar suka ga kungiyar sa Idon, wadda ta fara aiki makonni biyun da suka wuce, kan yadda ta gaza dakatarwa ko fitowa ta soki yadda dakarun tsaron gwamnati ke amfani da karfi a kan masu zanga zanga.

Karin bayani