Amnesty ta yabawa masu zanga-zanga a kasashen Larabawa

Hakkin mallakar hoto a
Image caption Tambarin kungiyar Amnesty International

A wani rahotan data fitar kan boren da aka gudanar a Kasasahen larabawa a shekarar 2011, kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta yabawa masu zanga-zanga a daukacin yankin larabawan, tana mai cewar sun yi tasiri sosai wajen kawo canji a yankunansu fiye da Kasashen duniya.

Rahotan ya ce ba za a yaudari masu fafutukar ba, da wasu sauye- sauye da ba zasu kawo wani canji na kirki ba ga rayuwarsu.

Wakilin BBC ya ce Amnesty ta kuma ce kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da kungiyar tarayyar turai da majalisar dinkin duniya da kungiyar kassahen larabawa sun gaza, ganin cewar basa daukar kwararan matakan kare hakkin dan adam kamar yadda suke yi a wasu Kasasahen daban.

A wani labarin kuma, Ministocin kungiyar kasasahen larabawa dake taro a birnin Alkahira na Kasar Masar sun amince da cigaba da aikin sa ido a Syria, da kuma kara yawan masu sa idon.

Tawaggar kassahen larabawan ta soma aikin tane makonni biyu da suka gabata, kuma 'yan adawar Syrian sun zargi tawaggar da kasa yin allawadai da kisan da jami'an tsaron kasar ke yiwa masu zanga- zangar nuna kin jinin gwamnati.