An kai hare hare a jihohin Edo da Zamfara

Hari a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hari a Najeriya

Wasu matasa sun kai hari a wani masallaci da ke birnin Benin na jihar Edo, sun kuma lalata shi.

Rahotanni sun ce, matasan sun raunata 'yan arewa da dama mazauna birnin, bayan sun yi wasoson dukiya mai dimbin yawa.

Wannan dai ana hangen wani martani ne matasan suka mayar, game da hare-haren da ake zargin 'yan kungiyar nan ta Boko Haram da kai wa coci-coci da 'yan asalin kudancin Najeriyar da ke zaune a arewacin kasar.

Can kuma a jahar Zamfara, hukumomin 'yan sanda sunce, sun kama mutane 19 ya zuwa yanzu, bayan wani hari da aka kaiwa wata coci da kuma fadar gwamnatin jihar a yau, a cikin zanga-zangar nuna rashin amincewa da janye tallafin man.

Kwamishinan 'Yan sandan jahar ta Zamfara, Tambari Yabo Mohammad, yace ba wanda aka raunata a harin da aka kaiwa Ebenezer Baptist Church da ke Gusau, sai dai an farfasa tagoginta da kuma kakkarya kujeru. Kwamishinan watsa labaran jahar, Ibrahim Muhammad, ya shaidawa BBC cewar gwamnati ta kafa dokar hana fitar dare a garin na Gusau har sai abinda hali yayi.

Karin bayani