An yakewa Hekmat hukuncin kisa

Hakkin mallakar hoto AMIRPRESS
Image caption Amir Mirza Hekmat

Wata kotu a Tehran ta yankewa wani Ba Amurka dan asalin Iran hukuncin kisa, bayan ta same shi da laifin leken asiri.

An kuma sami Amir Mirza Hekmati ne da laifin danganta Iran da ayyukan tada'adnaci.

A watan jiya ne gidan telbijin din Iran ya nuno Mr Hekmati wanda tsohon sojan Amurka ne yana amsa laifin sa.

Yace "da suka gano cewa ina dan jin larabci da kuma farisanci sai suka ce, zamu tura ka jami'a ka koyi larabci".

Mr Hikmati yana da kwanaki 20 don daukaka kara.

Iyalansa a Amurka sun ce yana ziyartar kakanninsa ne a kasar lokacinda aka tsare shi

Karin bayani