Libya ta hana ICC bayanai a akan Saif al Islam

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kama Saif al Islam ne a kudancin kasar

Kotun hukunta manyan laiffuka da ke Hague ta ce mahukunta a Libya basu amsa bukatar ta ba na neman bayanai game da lafiyar dan marigayi kanal Gaddafi wato Saif al Islam.

Kotun ta ce wa'adin da ta ba, mahunka a kasar zai cika ne a yau.

Sojojin dake adawa da Marigayi kanar Gaddafi ne dai su ka kama Saif al Islam a kudancin Libya a watan Nuwamban bara.

Kotun dai ta tuhume shi da wasu laifukka amma sabbin shugabannin na kasar Libya sunce zai gurfana ne a gaban kotu a kasar.

Kotun Hukunta manyan laifuka ta duniya dai ta bukaci gwamnatin Libya da ta bata damar ganawa da Saif al Islam.

Kotun tace tana so ta san halin da yake ciki. Har wa yau kotun ta ce tana son ta sani ko gwamnatiN Libya za ta mika shi domin ta tuhume shi. Yanzuwa yanzu dai kotun ta ce bata samu amsa a hukumace daga gwamnatin Libya ba a kan batun.

Idan har wa'adin da kotun da dibarwa Mahukunta a Libya ya cika a yau, akwai yiwuwar, Kotun za ta kai karar kasar, kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Ana dai tsare ne da Saif al Islam a Zinta dake kudu maso yammacin kasar.

A wata ziyara da wasu jami'an Kungiyar Human Rights Watch su ka kaimasa, Saif ya ce ana kula da shi yadda ya kamata amma sai dai an hana shi ganawa da Lauyoyinsa, kuma har yanzu ba a nuna mai tuhumce tuhumcen da ake yi masa ba.