Yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya

Yajin aikin ma'aikata a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban daruruwan ma'aikata ne suka yi yajin aikin ma'aikata a Najeriya

Mun kawo karshen bayanan da muke kawo muku kai tsaye kan yajin aikin kungiyoyin kwadago a Najeriya. Muna godiya da irin bayanan da kuka aiko mana. Da fatan za a ci gaba da kasancewa da sashin Hausa na BBC. Kada a manta da bbchausa.com/mobile.

Bayanan da muka kawo muku:

18:14 "Jami'an 'yan sanda a Kano sun ce mutum guda ya rasa ransa", amma majiyar asibiti ta tattabatarwa da BBC mutuwar mutane biyu, yayin da wakilinmu ya ce wasu mazauna birnin sun ce mutane hudu ne aka kashe a zanga-zangar.

17:26 Mahukunta a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya sun sanya dokar hana zirga-zirga daga karfe shida na yamma zuwa takwas na safe sakamakon tashin hankalin da aka samu a lokacin zanga-zangar adawa da janye tallafin man fetur.

17:02 A sakon da ya aiko mana ta email Musa Aliyu daga ya ce: "An gudanar da zanga-zangar kin amincewa da janye tallafin man fetur cikin lumana a jihar Naija. Masu zanga-zangar hade da kungiyar kwadago da sauran jama'a ne suka yi cincirindo a majalisar dokokin jahar, kasuwanni da shaguna da asibitoci da tashar motocin sun kasance a rufe".

16:13 Masu zanga-zanga a jihar Katsina sun ce za su yi zaman dirshen a gaban fadar sarkin garin har sai gwamnati ta janye matakin da ta dauka na janye tallafin man fetur.

15:22 An kai hari kan Hausawa mazauna birnin Benin a jihar Edo dake kudancin Najeriya. Kuma mutane kimanin goma sun jikkata a sanadiyyar harin, yayin da aka lalata wani masallaci. A halin yanzu Hausawa da dama ne ke zaman gudun hijira a barikokin 'yan sanda da na soji a Benin.

15:06 Cikakkun rahotannin rediyo kan yajin aiki a Najeriya yanzu haka a shashin Hausa na BBC http://www.bbc.co.uk/hausa/audio_console.shtml?programme=shirinrana

15:00 Ministan sadarwa na Najeriya Mr Labaran Maku ya yi kira ga kungiyar kwadago da su kawo karshen yajin aikin da suka fara. Mr Maku ya shaida wa BBC cewa gwamnati na daukar matakan ragewa jama'a radadin cire tallafin man.

14:54 A sakon da ya aiko mana ta facebook Halliru Usman Muhammad cewa yayi: "Muma anan Zamfara komi ya tsaya cik ko'ina matasa harma da dattijai dauke da ganye suna nuna goyon baya ga kungiyar kwadago. Ya kamata gwamnatin ta sauko daga matsayinta.

14:44 Akalla mutum guda aka kashe a zanga-zanga a Legas, yayin da wasu mutane uku suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga.

14:26 A sakon da ya aiko mana ta facebook, Bashir Farouq Sly-Dumber ya ce:"Wai ana zanga-zanga a wasu sassan Najeriya amma anan Warri jihar Delta ana ta hada-hadar mai, me ye ke faruwa ne?"

14:10 A sakon da ya aiko mana ta email daga Yobe, Aliyu Halilu cewa yayi: "Don Allah jami'an tsaro a Najeriya ku daina harbe mana yan'uwa masu zanga-zanga, saboda sun fito nuna alhininsu akan janye tallafin man fetur mana.

13:55 Wakilin BBC a Abuja Ibrahim Isa ya ce wasu daga cikin 'yan Majalisar wakilai ta kasa sun shiga sahun masu zanga-zangar adawa da janye tallafin man fetur din.

13:49 Wakilinmu a Kaduna Nura Muhammad Ringim ya ce jamian tsaro sun yi amfani da Barkonon tsohuwa wajen tura masu zanga-zangar baya a gidan gwamnatin jahar. Masu zanga-zangar sun yi wa fadar gwamnatin kawanya.

13:24 Daya daga cikin masu zanga-zanga a Kaduna Yusuf Umar, ya shaida wa BBC cewa sun yi wa fadar gwamnatin jihar kawanya domin nuna rashin amincewarsu da janye tallafin man fetur.

13:22 Shugaban kungiyar kwadago ta NLC Abdulwaheed Umar ya ce 'yan sanda sun kashe wani zanga-zanga a birnin Legas, yayin da wasu 14 ke samun magani a asibiti a Kano.

13:07 Kungiyar agaji ta Red Cross a jihar Kano, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "akalla mutane 14 ne ke samun magani a asibiti. Bakwai daga cikinsu an harbe su ne da bindiga".

12:41 Wakilinmu Abba Muhammad Katsina ya ce matan aure da kananan yara sun fito kan tituna domin zanga-zangar lumana kan janye tallafin mai a birane da kauyukan jihar Katsina.

12:28 Rahotanni sun ce an harbe mutum guda har lahira daga cikin masu zanga-zangar a Legas. Yayin da mutane goma suka samu rauni a tarzomar da aka yi a jihar Kano inda 'yan sanda suka harba hayaki mai sa hawaye.

12:18 A sakon da ya aiko mana ta email Mustafa Adamu ya ce: "Abin na da ban mamaki yadda shugaban kasan Najeriya da mashawartansa suka yi kunnen uwar shegu da kiraye-kiyayen da jama'a ke yi na a juya cire tallafin da suka yi.

12:11 Rahotanni sun ce jami'an tsaro sun harba barkonon tsohuwa sannan suka yi harbi a sama domin tarwatsa dubban masu zanga-zangar da suka taru a gaban gidan gwamnatin jihar.

12:07 Rahotanni daga jihar Kaduna sun ce tsohon gwamnan jihar a lokacin jamhuriya ta biyu Alhaji Balarabe Musa da kuma dan fafutukar kare hakkin bil'adama Shehu Sani, su ne suke jagorantar dubun-dubatar masu zanga-zanga. Yayin da a Kano manyan malaman jami'a suka fito domin baiwa masu zanga-zangar goyon baya.

12:00 A sakon da ya aiko mana daga Maiduguri, Isiaka Audu cewa yayi: Anan Maiduguri babu zanga-zanga, amma komai ya tsaya cak ba zirga-zirgar motoci, shaguna da kasuwa sun kasance a rufe.

11:47 Adadin jama'ar da suka fito zanga-zanga sai kara karuwa yake yi a sassan Najeriya da dama. Daga Legas zuwa Kano, Kaduna, Abuja, Katsina, Sokoto, Bauchi, Edo, Benue da Nassarawa. Masu zanga-zangar na dauke da kwalayen da ke nuna rashin amincewa da janye tallafin man fetur. Gwamnati ta ce za ta yi amfani da kudaden ne wajen inganta rayuwar 'yan kasar.

11:31 Rahotanni sun ce babu wata zirga-zirga ta azo-agani a filayen saukar jiragen sama na Legas da kuma na Abuja sakamakon yajin aikin kungiyoyin kwadago. An jibge jami'an tsaro da dama suna gadin filayen jiragen sama tare da hana mutane shiga.

11:25 "Ya kamata shugaban kasa ya duba halin da talakawan kasar sa suka shiga dalilin janye tallafin man fetur". A cewar Ismail Idriss Potiskum

11:24 A sakon da ya aiko mana daga Katsina ta email Kabir Sirajo yace: shaguna na cikin gari a kulle, kwata a kulle, ga 'yan zanga-zanga tare 'yan-sanda a cikin gari.

11:17 Rahotanni daga jihar Kaduna sun ce dubun-dubatar mutane ne suka fito domin zanga-zangar adawa da cire tallafin man, kuma al'amura na tafiya lami-lafiya.

11:11 Gwamnatin Najeriya ta ce ta janye tallafin mai ne domin ta samu kudaden da za ta gudanar da ayyukan ci gaban kasa. Ta kara da cewa wasu tsirarin mutane ne ke amfana daga tallafin ba wai talakawa ba.

11:03 Rahotanni sun ce yajin aiki da zanga-zanga na ci gaba a jihohin Nassarwa da Naija da Kogi. Yayin da adadin mutanen da suka fito zanga-zanga ke ci gaba da karuwa a jihohin Legas da Kano da kuma birnin Abuja.

10:32 An jibge jami'an tsaro a sassan Najeriyar da dama domin a tabbatar cewa ba a samu tashin hankali ba. Rahotanni sun ce matasa na hana masu ababen hawa kaiwa-da-komowa a Legas.

10:27 Jagoran kungiyar Save Nigeria, kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta CPC a zaben watan Afrilu Mr Tunde Bakare, ya yi jawabi ga masu zanga-zanga a Ojota Legas: "Wajibi ne mutane su tashi tsaye su kwatowa kansu 'yanci".

10:22 A sakon da ya aiko mana ta shafin facebook, Ali Suleiman Muhammad cewa yayi: Mu kan Kano muna cikin yajin aiki da zanga-zangar limana. Kuma ko'ina kantuna a rufe da kasuwanni da bakuna da ma'aikatu da masa'antu.

10:10 Bayanai daga sassan Najeriya da dama sun nuna cewa ma'aikatun gwamnati da bankuna da wasu kasuwanni sun kasance a rufe, yayin da jama'a ke ci gaba da zaman dirshen a gidajensu, wasu kuma na fita domin zanga-zangar da suka yi wa lakabi da 'mamaye Najeriya, wato Occupy Nigeria a Turance.

10:03 A sakon da ya aiko mana ta shafin facebook Ahmad B Sani Dogarawa Zaria ya ce: Jonathan mu talakawa bama son kudirin da ka dauka don haka ka gaggauta mai da hannun gwamnati a harkan man fetur ko kuma ka fuskanci turjiya daga talakawanka na yin zanga-zangar sai baba-ta-gani.

09:54Jama'a da dama sun fara taruwa a dandalin Gani da ke birnin Legas domin zanga-zanga, yayin da a Abuja babban birnin kasar ma jama'a suka fara hallara a shataletalin Berger domin gudanar da zanga-zangar adawa da janye tallafin man fetur.

09:37 Ma'aikata da dama a Najeriya sun kasance a gidajensu domin amsa kiran da kungiyoyin kwadago suka yi na yajin aiki.

Karin bayani