'Yan Najeriya sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga zanga a birnin Lagas

Dubban 'yan Najeriya su ka shiga yajin aikin gama-gari na sai baba-ta-gani.

Ma'aikatan gwamnati dana kamfanoni masu zaman kansu, na bukatar gwamnatin Najeriya ta dawo da tallafin man da take bayarwa wanda tace ta janye a makon da ya gabata.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce wannan wani mataki ne na tsuke bakin aljihu da kuma yaki da almundahana.

Tunda gwamanatin ta janye tallafin dai, farashin man fetur ya nunka a Kasar, wanda hakan yasa da dama daga cikin al'ummar Kasar su sama da Miliyan 160 da suke rayuwa akan kasa da dalar Amurka biyu a rana kara shiga cikin kuncin rayuwa.

Tuni dai Majalisar wakilan kasar ta bukaci gwamnati da ta jingine matakin janye tallafin man petur.

A lokacin wani zaman gaggawa da Majalisar ta yi a ranar Lahadi ta ya nemi da a kara tattaunawa kan matakin da gwamnatin ta dauka, wanda ya sa farashin mai ya ninka.

Gwamnati ta kare matakin ta

Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonthan, ya kare matakin da ya dauka na janye tallafin man fetur, inda ya ce ya dauki matakin ne don inganta tattalin arzikin kasar.

Tun bayan sanarwar janye tallafin a makon da ya gabata dai, farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi.

A jawabinsa na mai da martani a hukumance na farko, shugaban kasar ya yi kira ga 'yan Najeriya su goya masa baya:

''Zan so in yi amfani da wannan dama in tabbatarwa 'yan Najeriya cewa ni ma fa ina jin irin radadin da dukkanku ke ji na hauhawar kudin mota da farashin kayayyakin masarufi''.

Shugaban kasar ya kuma ba da sanarwar rage albashin manyan ma'aikatan gwamnati da kashi ashirin da biyar cikin dari, da kuma soke tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, sai dai wadanda suka zama dole.

Karin bayani