An shiga rana ta biyu da yajin aiki a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga zanga a Najeriya

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun shiga rana ta biyu soma yajin aikin ma'aikata game da tsadar man fetur, wanda cire tallafin man ya haifar.

Ofisoshi da kantina da makarantu a daukacin Kasar sun kasance a rufe a ranar Litinin .

An kuma ruwaito cewar an kashe akalla mutane uku a lokacin wata taho- mu- gama tsakanin masu zanga -zangar da kuma 'yan sanda.

Yajin aikin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman dar- dar sakamakon Kashe kashen dake cigaba da aukuwa a sassa daban- daban na Kasar.

An ruwaito cewar dubun - dubatar musulmi 'yan arewacin Najeriya nata komawa gida daga kudancin Kasar, yayinda Kiristoci dake arewacin Kasar suma suke ta komawa yankunansu na asali.

A wata hira da yayi da BBC, Marubucin nan dan Najeriya Wole Soyinka, yayi kira da a gudanar da wani taro na Kasa domin magance halin da ake ciki

Ya ce akwai wasu shugabanni a wasu sassan Kasar da suke jin cewa, ba za su amince da duk wani addini ba, bacin nasu.

Karin bayani