An wanke gwamnatin Rwanda daga zargin kisa

Shugaban Rwanda Paul Kagame Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Rwanda Paul Kagame

Gwamnatin Rwanda ta yi marhabun da wani rohoton da Faransa ta fitar dake nuna cewa, wasu 'yan Hutu masu tsatsauran ra'ayi ne suka harbo jirgin saman shugaban kasar a 1994.

Wannan ne ya haddasa kisan kiyashin kasar inda aka hallaka mutane dubu 800, galibi 'yan kabilar Tutsi.

Rohotannin da aka fitar akan lamarin a baya dai sun dora laifin ne akan 'yan tawayen Tutsi, a karkashin jagorancin shugaban kasar na yanzu, Paul Kagame.

An dade ana ta samun bayanai masu cin karo da juna akan wanda ya kashe tsohon shugaba Juvenal Habyarimana.

Karin bayani