Kwana na 2 na yajin aiki a Najeriya

Ana zaman dar-dar a wasu sassan Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mai zanga-zanga a birnin Legas na Najeriya

Ana ci gaba da zaman dar-dar a rana ta biyu ta yajin aikin gama-gari da ake yi da kuma wasu tashe-tashen hankula da aka yi fama da su a wasu sassan kasar.

'Yan sanda sun yi amfani da barkonan tsohuwa domin yin bata-kashi da masu zanga-zanga wadanda suka yi kokarin mamaye fadar gwamnatin jihar Kaduna.

Wakilin BBC Nura Muhammad Ringim ya ce an harbi mutum guda daga cikin masu zanga-zangar.

Rahotanni daga jihar Naija na cewa masu zanga-zanga sun datse hanyar dake zuwa Minna babban birnin jihar daga Abuja ta bagaren lambata.

Masu aiko da rahotanni sun ce ana zaman dar-dar a birnin Legas bayan da aka kashe wani mai zanga-zanga a ranar Litinin sakamakno zanga-zangar adawa da cire tallafin man fetur.

Kungiyoyin kwadago a birnin Kano sun dakatar da gudanar da zanga-zanga bayan da aka kashe mutane biyar.

Jama'a a birnin na Kano sun kasance a cikin gidajensu biyo bayan tashin hankalin da aka yi a ranar Litinin - sai dai rahotanni sun nuna cewa wasu sun fita domin neman na abinci.

An gudanar da zanga-zanga a Abuja

Yawancin al'amura sun tsaya cak a kasar, ciki harda asibiti.

An gudanar da zanga-zanga a Abuja babban birnin kasar, inda shaguna da makarantu da gidajen mai suka kasance a rufe.

Kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ce 'yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye da kuma harsashi sama a garin Bauchi. Sai dai babu wanda ya jikkata.

Wakilin BBC Mark Lobel a Legos ya ce darajar kasuwar hannayen jari ta Najeriya ta fadi da kashi biyar idan aka kwatanta da yadda take a ranar Litinin, sai dai kamfanonin mai sun ce ana ci gaba da ayyukan hako mai.

Wasu masu zanga-zangar sun yi mutun-mutumin shugaba Jonathan inda suka yi masa lakabi da "Badluck" wato rashin nasara.

Farashin mai ya ninka

A jihar Kano, an kafa dokar hana zirga-zirga daga karfe shida na yamma zuwa takwas na safe bayan mummunar arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro.

Jami'an kungiyar kwadago a birnin sun ce ba za a sake gudanar da zanga-zanga ba, amma yajin aiki zai ci gaba, a cewar wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai.

Sai dai a zaman da ta yi bayan ta dawo daga hutu, Majalisar dattawan Najeriya ta kasa fayyace matsayinta a kan matakin da gwamnatin kasar ta dauka na janye tallafin man fetur din.

Sai dai ta bayyana cewa ta kafa kwamiti na musamman don tuntubar bangaren zartarwa da kungiyar kwadagon kasar da nufin samar da masalaha game da yajin aikin gama-gari da ake yi a kasar.

Tuni dai bangaren majalisar wakilan kasar ya nemi gwamnati da ta dawo da tallafin da take bayarwa a bangaren man fetur, domin 'yan kwadago su janye yajin aikin.

Farashin mai da na sufuri sun ninka tun ranar 1 ga watan Janairu loakcin da aka sanar da janye tallafin.

Yawancin 'yan kasar na ganin wannan ne kawai abinda suke amfana daga gwamnati.

Duk da cewa kasar na sahun gaba wajen hako danyan mai a duniya, bata da ingantattun matatan man fetur, don haka take shigo da tataccen mai daga waje.

Karin bayani