An kashe wani masanin kimiyyar Iran

An kashe wani masanin kimiyyar Iran
Image caption Iran ta dora alhakin kisan kan kasashen Amurka da Isra'ila

Iran ta ce wani masanin kimiyya wanda ke aiki a daya daga cikin tashoshin nukiliya na kasar ya mutu sakamakon tashin wani bom a Tehran, babban birnin kasar.

Wasu rahotanni daga Iran din sun ce wasu mutane ne a kan babur suka lika wani abu mai magana disu a jikin motar mutumin.

An bayyana cewa sunan marigayin Mostafa Ahmadi Roshan, kuma yana aiki ne a tashar inganta makamashin uranium da ke Natanz.

Iran ta dora alhakin harin, wanda shi ne na baya-bayan nan a jerin hare-haren da ake kaiwa kan masana kimiyya na Iran din, a kan hukumomin leken asiri na Amurka da Isra'ila.

Wani malami a jami'ar Tehran Farfesa Sadeq Zimbakalam, ya ce "ina ganin ba shakka cewa hukumar leken asiri ta Mossad da jami'an leken asiri na Isra'ila ne ke aikata wadannan kashe-kashen".

Karin bayani