An yi barazanar hana ma'aikata albashi a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Gwamnatin Najeriya ta yi gargadin cewa duk wani ma'aikaci da ya ci gaba da shiga yajin aikin da kungiyar kwadagon ta kira, ba za a biya shi albashi ba.

Wata sanarwa data fito daga Ministan shari'ar kasar, ta kuma bukaci kungiyar kwadagon da tabi umarnin kotun warware rikici tsakanin ma'aikata da gwamnati, wacce ta bada umarnin kada kungiyoyin kwadagon su gudanar da yajin aikin.

Mista Muhammed Bello Adoke ya fitar a jiya, ya tunatar da kungiyoyin kwadago a kasar da cewa kotun ma'ikata ta haramtawa kungiyoyin shiga yajin aiki, har sai ta saurari karar da gwamnatin tarraya ta shigar mata.

Harwa yau ya ce kotun tana da ikon hana kowacce kungiya shiga yajin aiki kamar yadda dokar kasar ta bata hurumin shiga tsakanin a harkoki ma'ikata da gwamnati.

Mista Adoke ya ce kotun ta sanya gobe alhamis ne domin sauraran karar da gwamnati ta shigar kan kungiyoyin kwadagon kasar saboda barazanar shiga yajin aikin da ta yi tunfarko.

A kan haka ne dai Ministan Shari'ar ya yi kira da ma'ikatan gwamnati da ma masu zaman kansu da su dawo bakin saboda yajin aikin da kungiyar kwadago ta shiga baya kan ka'ida.

Mista Adoke ya yi gargadin cewa duk ma'aikacin da ya ki dawowa kan aiki ba zai samu albashi ba.

Ya ce gwamnati za ta tabbatar da kare duk ma'ikata da sauran 'yan kasa a yayinda suke dawowa bakin aikinsu.

Ministan Shari'ar ya ce gwamnati ta damu matuka da rayuka da aka rasa a 'yan kwanakin da aka kwashe ana zanga zanga, inda ya ce Ofishinsa da Hukumar kare hakin bil'adama da kuma Hukumar 'yan sanda za su sa'ido domin ganin an daina amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga zanga da kuma kare lafiyar jama'a.

Karin bayani