Jama'a na ci gaba da zanga zanga a Najeriya

Masu zanga zanga a Najeriya Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Masu zanga zanga a Najeriya

Ana cigaba da yajin aiki da kuma zanga zanga a sassa dabam dabam na Najeriyar, domin kokawa da cire tallafin man petur din da gwamnati ta yi.

Tun shekaranjiya Litinin ne kungiyoyin kwadago da sauran jama'a suka fara daukar wannan matakin.

A wasu jihohi an kafa dokar hana fita, sakamakon tashe tashen hankulan da suka faru a lokacin zanga zangar, kuma an sami hasarar rayuka da kuma jikkata a wurare dabam dabam.

Gwamnatin Najeriya dai ta yi gargadi ga ma'aikatanta cewa ba za a biya su ba idan ba su koma bakin aiki ba.

Karin bayani