An sallami sakataren tsaron Pakistan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Firayim Ministan Pakistan, Yusuf Raza Gilani, ya sallami sakataren tsaro na kasar, Laftanar Janar Khalid Lodhi, yana zargin sa da aikata ba-daidai ba.

Wannan mataki dai ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ta da jijiyoyin wuya tsakanin gwamnati da rundunonin sojin kasar.

Tun da farko dai a ranar Laraba rundunonin sojin sun soki Firayim Ministan akan wata hira da ya yi da kafofin yada labarai kwanan nan.

A hirar dai Mista gilani ya zargi hafsan hafsoshin sojin da kuma shugaban hukumar leken asiri ta kasar da keta doka ta hanayr ba da shaida yayin wani bincike da Kotun Kolin kasar ke gudanarwa.

Karin bayani