Ma'aikantan mai sun yi barazanar shiga yajin aiki a Najeriya

Image caption Daruruwan 'yan Najeriya da su ka fito zanga zanga

A yayinda aka shiga rana ta hudu, Kungiyar ma'aikatan mai mafi girma a Najeriya tayi barazanar dakatar da aikin hakar man, matukar har gwamnatin Kasar bata dawo da tallafin da take baiwa bangaren mai ba.

Cire tallafin man dai ya janyo farashin man ya nunka a Kasar, abinda ya haddasa yajin aiki a fadin Kasar, inda a yau ake shiga rana ta hudu.

Kungiyar ta PENGASSAN ta ce tana shirin shiga yajin aikin, amma ta ce tana fatan gwamnatin Najeriyar ba zata bari lamarin ya kai nan ba.

Gwamnatin Najeriya dai na dogaro ne da fitar da danyan man wajen samun kudaden shigarta.

Ya zuwa yanzu dai yajin aikin da ake yi, bai dakatar da aikin hakar man ba

Kin biyan albashi

Da alamu barazanar da gwamnatin tarayyar ta yi wa ma'aikatan da su koma bakin aikinsu ko kuma su rasa albashinsu bai yi tasiri ba.

Ma'aikata dai sun yi burus da umarnin, abin da yasa ma'aikatun gwamanti da harkokin kasuwanci suka ci gaba da kasancewa a rufe a galibin jihohin kasar.

Sai dai sabanin hasashen da wasu keyi a da cewar zanga-zangar da ake yi ka iya share hanyar rabewar kasar biyu, a daya hannun zanga-zangar, ta yi dalilin hada kan wasu 'yan kasar wuri guda, ba tare da la'akari da bambancin addini ko kabila ba.

Gwamnati da Kungiyoyin kwadago dai sun ce su na ci gaba da tattaunawa domin samu maslaha game da batun.

Karin bayani