Jonathan na ganawa da kungiyoyin kwadago

Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Goodluck Jonathan na fuskantar matsin lamba daga sassa da dama

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya fara tattaunawa da wakilan kungiyar kwadago domin kawo karshen yajin aikin gama-garin da ake yi wanda ya tsayar da al'amura cik a kasar.

Wakilin BBC a Abuja Ibrahim Isa ya ga lokacin da tawagar kungiyar 'yan kwadagon ta isa fadar shugaban kasar domin halartar tattaunawar.

Kuma daga nan ne suka shiga tattaunawar sirri da shugaba Jonathan wanda tun da farko ya gana da gwamnoni 36 na kasar.

Kungiyoyin kwadagon wadanda ke da gagarumin goyon bayan jama'ar kasar, sun shiga yajin aiki ne domin nuna adawa da matakin gwamnati na janye tallafin man fetur.

Kungiyar ma'aikatan man fetur ta kasar ta yi barazanar toshe hanyoyin hakowa da fitar da danyan mai daga ranar Lahadi idan gwamnati bata sauya matsaya ba.

Jonathan na fuskantar matsin lamba

Jami'an gwamnati da masana tattalin arziki sun ce janye tallafin zai samarwa da gwamnati dala biliyan 8 a kowacce shekara domin gudanar da ayyukan ci gaban kasa.

Shugaban babban bankin kasar Sanusi Lamido Sanusi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa kasar na yin asarar naira biliyan 100 a kowacce rana sakamakon yajin aikin da 'yan kwadagon suke yi.

Rikicin addini da na kabilanci a sassan kasar da dama ya kara cakuda al'amura a kasar da ke da yawan mabiya addinin Musuluci da kuma na Kirista.

Shugaba Goodluck Jonathan na fuskantar matsin lamba daga fuskoki daban-daban domin ya shawo kan halin da kasar ta samu kanta a ciki.

Masana na hasashen idan har ba a dauki wani mataki cikin gaggawa ba, to al'amura za su iya fin karfin gwamnatin.

Tuni dai aka sanya dokar tabaci da ta hana zirga-zirga a wasu jihohin kasar da dama domin shawo kan tashin hankalin da ake alakantawa da Boko Haram ko kuma wanda ya biyo bayan zanga-zangar adawa da cire tallafin man fetur.

Karin bayani