Farashin danyen mai ya tashi saboda tashin hankali a Najeriya

Farashin danyen man fetur ya tashi sakamakon tashe-tahsen hankula a Najeriya da kuma barazanar sanyawa Iran takunkumin fitar da mai zuwa waje.

A kasuwannin nahiyar Asiya farashin ya tashi da centi sittin ya kai fiye da dala dari da daya ko wacce ganga.

Kungiyar ma'aikatan man fetur mafi girma a Najeriya, PENGASSAN, ta yi barazanar za ta dakatar da aikin hako man idan gwamnati ba ta mai da tallafin da ta janye ba.

Janye tallafin dai ya sa farashin man fetur ya nunka fiye da sau biyu, ya kuma haddasa yajin aikin gama-gari wanda ya shiga kwana na hudu yau.

Karin bayani