Rana ta hudu ta yajin aiki a Najeriya

Rana ta hudu ta yajin aiki a Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dubban Jama'a ne suka fito domin zanga-zangar adawa da matakin gwamnatin

Mun kawo karshen bayanan da muke kawo muku kai tsaye game da abubuwan da suka faru a rana ta uku ta yajin aikin gama-gari da zanga-zanga da kungiyoyin kwadago suka kira domin nuna adawa da janye tallafin man fetur. Mun gode da gudummawar da kuke bamu, sai a ci gaba da kasancewa da sashin Hausa na BBC.

16:45 Mun kawo karshen bayanan da muke kawo muku kai tsaye game da abubuwan da suka faru a rana ta uku ta yajin aikin gama-gari da zanga-zanga da kungiyoyin kwadago suka kira domin nuna adawa da janye tallafin man fetur. Mun gode da gudummawar da kuke bamu, sai a ci gaba da kasancewa da sashin Hausa na BBC.

16:23 Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin a kame jami'in dan sandan da yayi harbi kan masu zanga-zanga a jihar. Rahotanni sun ce mutane biyu ne aka harba inda yanzu haka suke karbar magani a asibiti.

14:53 "Labarin da muka samu daga jihar Kaduna na cewa gwamnatin jihar ta yi sassauci akan dokar hana zirga-zirga, inda yanzu jama'a za su iya fita daga karfe daya na rana zuwa karfe biyar na yamma".

14:50 Kungiyar ma'aikatan man fetur a Najeriya ta sha alwashin rufe wuraren hakar man fetur a kasar daga ranar Lahadi, idan har gwamnati bata janye matakin da ta dauka na cire tallafin man fetur ba. Har yanzu dai ana ci gaba da kokarin shawo kan kungiyoyin kwadago da kuma bangaren gwamnati.

14:39 A Najeriya wata kungiya mai suna Niger Delta Movement for Radical Change, ta baiwa 'yan arewacin kasar da ke zaune a yankin Niger Delta, wa'adin makwanni uku na su san inda dare yayi masu - idan ba haka ba za ta kai masu hare-hare.Kungiyar ta yi barazanar ce, a cikin wasikar da ta aikewa 'yan arewar a ranar Laraba.

14:18 Rohotanni daga jihar Borno na cewa gwamntin jihar ta kafa dokar hana yawon dare a Maiduguri babban birnin jihar. Dokar za ta yi aiki ne daga karfe 5 na yamma zuwa karfe 7 na safe.Kwanishan yada labaran Jihar, Inuwa Bwala ya shaida wa BBC cewa dazu ne gwamnatin jihar ta bada sanarwar kafa dokar a wani matakin tabbatar da tsaro a jihar.

13:46 Rahotanni sun ce 'yan sandan dake sunturi a unguwar Kurna sun yi harbi kan wasu masu zanga-zanga a Kano, inda ake ce an harbi mutane biyu da yanzu haka ke karbar magani a asibiti.

12:53 Rahotannin da muke samu sun nuna cewa 'yan Majalisun kasa a Najeriya na kokarin sasanta tsakanin kungiyoyin kwadago da kuma bangaren gwamnati domin kawo karshen yajin aiki da zanga-zangar da ake yi a kasar. Sai dai kawo yanzu ba a kai ga cimma wata matsaya ba.

12:40 A wani mataki makamancin na gwamnatin Najeriya, kasar Uganda ta janye tallafin da take bayarwa kan fannin wutar lantarki. Sanarwar da gwamnatin ta fitar na nufin cewa a yanzu farashin wutar lantarkin zai karu da kusan kashi 42 cikin dari.

12:15 A jihar Legas ma dubban jama'a ne suka sake fitowa kan tituna a rana ta hudu ta yajin aiki da zanga-zanga domin nuna adawa da matakin gwamnatin kasar na janye tallafin mai. Ana gudanar da jawabai da ke kara nuna bijirewa ga matakin gwamnatin kasar.

11:58 Hukumar kiyaye hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce ayyukan kungiyar Boko Haram ta Najeriya za su iya kasance wa na cin zarafin bil'adama. Shugabar hukumar Navi Pillay, ta fada a wata sanarwa cewa idan aka samu mambobin kungiyar da kai hare-hare kan jama'a ta fuskar addini da kuma kabilanci, to za a iya hukunta su da laifin cin zarafin bil'adama.

11:38 "Rahotanni sun ce akalla mutane biyu ne aka harba yayin da aka nakadawa wasu 'yan sanda duka bayan da tarzoma ta barke tsakanin mazauna garin Gurara a jihar Naija da kuma 'yan sanda. Jama'a sun zargi 'yan sandan da bude wuta kan mazauna garin bayan takaddamar da ta barke sakamakon aiwatar da dokar hana fita da aka sanya a jihar. A yanzu dai komai ya lafa".

11:11 Wakilin BBC a Sokoto Haruna Shehu Tangaza, ya ce malaman addinin Musulunci a jihar na shirin gudanar da sallah da addu'o'i domin nuna adawa da matakin gwamnatin Najeriya na cire tallafin man fetur.

10:58 A Abuja babban birnin Najeriya kungiyar kwadago da sauran masu fafutuka sun ci gaba da fitowa kan tituna domin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi.

10:54 "Rahotannin da muke samu daga jihar Kano a Arewacin Najeriya na cewa dubban matasa sun mamaye kan titin Katsina inda nan ne ofishin kungiyar kwadagon jihar ya ke. Rahotanni sun ce komai na tafiya lami lafiya".

10:48 Sakon Muhammed Uba ta email "Ina kira ga 'yan uwana Musulmai da Krista da mu hada kanmu mu zauna lafiya. 'Yan Boko Haram ba Krista kadai suke kashewa ba har da Musulmai, Najeriya tamu ce. ALLAH ya bamu zaman lafiya".

10:44 A sakon da ya aiko mana ta email Iliyasu Akilu daga Maiduguri cewa yayi: "Mu a jihar Borno duk da hukumomi sun hana mu fitowa zanga-zanga zuciyar mu tana tare da shugabannin kwadago da sauran 'yan Najeriya dari bisa dari. Kuma muna taya su addu'a ALLAH ya taimake mu".

10:10 Farashin danyan mai a kasuwar duniya ya tashi da dala daya kan kowacce ganga a ranar Alhamis bisa tsoron cewa yajin aikin gama-gari da zanga-zanga a Najeriya da kuma sa'insa tsakanin kasar Iran da kasashen Yamma, zai iya kawo cikas a fannin hakar mai.

10:01 "An shiga rana ta hudu a zanga-zanga da yajin aikin gama-gari da kungiyoyin kwadago ke yi a Najeriya domin adawa da janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi. Gwamnati ta gargadi 'yan kwadago cewa ba za a biya duk am'aikacin da bai je aiki ba. Amma duk da haka shaguna da bankuna da makarantu da ma gidajen mai sun kasance a rufe".

Karin bayani