An saki fursunoni 651 a kasar Burma

burma
Image caption Fursunoni a Burma

Burma ta fara sako karin fursunoni, yayinda ake sa ran cewa daga cikinsu akwai bijirarrun yan adawa.

Mahukunta a kasar ta Burma sun bada sanarwar cewa, su na shirin sako bursunoni dari shidda da hamsin da daya.

Akwai kwararan rahotannin dake nuna cewa, daga cikin wadanda za a sako, har da tsohon Pirayi ministan kasar Khin Nyunt da kuma Ko Jimmy, sanannen jagoran daliban da suka yi zanga zanga a shekarar 1988, da kuma mabiya addinin buda dake gaba gaba wurin gudanar da zanga zangar adawa da gwamnati a shekarar 2007.

Wakiliyar BBC ta ce a cikin wata sanarwa da aka watsa ta kafafen yada labarun gwmanati, shugaban kasar Burma ya ce daga cikin wadanda za a sako har da wadanda za su taimaka wurin inganta zaben kasar.

An kiyasta cewar akalla mutane 600 zuwa 1000 ne ke tsare a gidajen yarin Burma.

Daga cikinsu akwai masu rajin kare demokradiya da masu ibadar budda da kuma 'yan jarida.

A farkon wannan watan ma an saki wasu fursinoni amma kuma babu fitattun 'yan siayasa a cikinsu amma kuma a wannan karon akwai alamun cewar za a samu sauyi.

Karin bayani