Amurka ta yi marhabin da sakin fursunoni a Burma

Wasu fursunoni da aka sako a Burma Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu fursunoni da aka sako a Burma

Amurka ta bayyana sakin wasu fitattun fursunonin siyasa a Burma da cewa wani muhimmin mataki ne na sauye-sauyen dimokuradiyya.

Shugaba Obama ya ce yin afuwa ga fursunoni kusan dari shida muhimmin mataki ne na hada kan kasa.

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce kasarta za ta fara daukar matakin musayar jakadu da kasar ta Burma.

Sai dai ta ce akwai bukatar kara tashio tsaye daga bangaren hukumomin Burman, ciki har da gudanar da zabubuka bisa gaskiya da adalci da kuma kawo karshen yakin da suke yi da 'yan tawaye.

Karin bayani