El-Baradei ba zai tsaya takarar shugaban kasa ba

Mohamed elbaradei Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mohamed Elbaradei

Daya daga cikin 'yan takarar zaben shugaban kasa a Masar, Mohammed el Baradei, ya bada sanarwar janye takararsa.

Mr el Baradei, wanda ya taba samun kyautar Nobel, kuma tsohon shugababn Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, ya ce har yanzu da sauran aiki a gaba kafin Demokradiyya ta zauna da gindinta a Masar.

Ya soki lamirion Majalisar mulkin sojan kasar, yana mai cewa tana gudanar da mulki ne, kamar ba'a yi juyin juya hali a kasar a bara ba.

Har yanzu dai majalisar mulkin sojan kasar ta Masar, ba ta tsaida ranar da za'a yi zaben shugaban kasar ba, amma ta ce za'a samu sabon shugaban kasa nan da karshen watan Yuni mai zuwa.

Karin bayani