Mutane shida sun mutu a Italiya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jirgin ruwan da ya yi hatsari a iltaliya

Rahotanni daga kasar Italiya na cewa akalla mutane shida ne suka halaka a lokacin da wani jirgin ruwa ya kubce ya hau gabar tekun da ke yammacin kasar.

Mutane fiye dubu hudu ne aka kwashe daga jirgin, wanda ke tafiya a tekun Mediterranean.

Kafafen yada labarai sun ruwaito fasinjojin da ke jirgin na cewa sun ji kara mai karfi kafin jirgin ya yi tangal-tangal, sannan ya tsaya, inda daga bisani wutarsa ta dauke.

Wasu rahotannin kuma na cewa wasu daga cikin fasinjojin jirgin mai suna Costa Concordia, sun yi tsalle suka fada ruwa.