An ceto wasu fasinjojin jirgi a Italiya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutanen da aka ceto daga cikin jirgin ruwan.

A kasar Italiya, an ceto fasinjoji biyu da ke cikin jirgin ruwan da ya kife da ransu, sao'i 30 bayan da ya kubce ya hau kan gabar tekun yammacin kasar .

An samu mutanen biyu ne, wadanda mata da miji ne 'yan kasar Korea, a makale jikin wani allon jirgin, sannan aka kai su inda ake ajiye wadanda suka tsira.

Sai dai har yanzu ba a san inda fasinjoji arba'in suke ba.

Jirgin ruwan mai suna Costa Concodia ya kife ne, ta yadda za a iya ganin wani fafakeken rami a gabansa, kusa da inda matukinsa yake.

Hakan ba ya rasa nasaba da tukunyar gabar tekun da ya yi.

An ceto kusan dukkan fasinjoji dubu hudun da ke cikinsa.

'Yan sanda sun kama direban jirgin, inda ake yi masa tambayoyi game da yadda jirgin ruwan ya tunkuyi gabar tekun, duk da yake kogin bai yi toroko ba.