An fara hako mai a Somalia

Hako mai a Somalia Hakkin mallakar hoto othar
Image caption Hako mai a Somalia

Wani kamfanin hakar mai na kasar Canada ya fara tono mai a Somalia, a karon farko da irin hakan ke faruwa cikin shekaru ashirin.

Kamfanin mai suna Horn Petroleum zai haka rijiyar mai a yankin dake da kwarya-kwaryar cin gashin kai na Puntland.

Yana kuma shirye-shiryen haka rijiya ta biyu kuma ya ce kowacce zata dau kusan watanni uku a kammala ta kuma fara aiki.

An dakatar da hakar mai a Somalia bayan da aka kifar da gwamnatin kasar a shekarar 1991.

Wakilin BBC ya ce a baya dai sa hannu kan kwangilar hakar mai ta jawo rikici da gwamnatin rikon kwaryar Somaliyan, tana mai cewa Puntland wadda ta balle ba ta da ikon sa hannu kan wata yarjejeniya da kamfanonin kasashen waje.

Babu wani mai da aka tabbatar Puntland na da shi, amma an ce yankin da ta ke kai daya yake da wanda ya tafi har zuwa kasar Yemen.

Karin bayani