Baraka ta kunno kai a kungiyar kwadago ta NLC

Baraka ta kunno kai a kungiyar kwadago ta NLC Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yan sanda sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zanga

Reshen jihar Kano na kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ya yi watsi da matakin da uwar kungiyar ta dauka na janye yajin aiki da zanga-zanga domin adawa da karin farashin man fetur a kasar.

'Yan kwadagon na Kano sun za su ci gaba da yajin aiki da kuma zanga-zanag duk kuwa da sanarwar da uwar kungiyar ta kasa tayi na janye yajin aikin da kuma zanga-zanga.

Shugaban kungiyar a Kano kwamarade Isa Yunusa Dan Guguwa wanda kuma dan kwamitin kolin kungiyar ne na kasa ya shaida wa wani taron manema labarai a Kano cewa ba a tuntube su ba lokacin da aka dauki matakin janye yajin aikin.

"Shugabannin kungiyar ne kawai a Abuja suka bada sanarwar, ba tare da tuntubar sauran shugabanni ba, wanda yace hakan ya sabawa matsayar da suka tashi a kanta".

Tun kafin bayar da sanarwar dubban dururuwan mutane a jihar sun fito kan tituna domin ci gaba da zanga-zanga karkashin jagorancin kungiyar kwadagon jihar, ciki kuwa harda mata da kuma tsofaffi.

Suma anasu bangaren kungiyoyin farar hula na kasar sun yi Allah wadai da matakin na kungiyar kwadago suna masu cewa za su ci gaba da zanga-zanga ba kakkauta wa.

A ranar Litinin da safe ne dai shugaba Goodluck Jonathan ya bayar da sanarwar rage farashin man daga naira 141 zuwa naira 97, sai dai kungiyoyin farar hula sun yi watsi da matakin suna masu kiran da a koma farashin asali na naira 65 kan kowacce lita.

Dr Jonathan ya kara da cewa gwamnati za ta tabbatar cewa gidajen mai sun yi biyayya ga sabon farashin.

Ya ce an rage farashin ne bayan ya tuntubi gwamnoni da shugabannin majalisar dokokin kasar, wandanda suka goyi bayansa akan batun.

Shugaba Jonathan ya yi ta'aziya ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin zanga-zangar adawa da janye tallafin mai, inda ya kuma jinjinawa wadanda suka gudanar da zanga zangar lumana.

An tsaurara matakan tsaro

Sai dai shugaban ya ce zai ci gaba da kokarin ganin an janye tallafin man baki daya.

Matakin na su na zuwa a daidai lokacin da ake zaman dar-dar a Legas bayan da sojoji suka yi harbi domin tarwatsa masu zanga-zanga a safiyar ranar Litinin. Tunda sanyin safiya ne jami'an sojin suka mamaye dandalin marigayi Gani Fawehinmi inda aka shafe mako guda ana zanga-zangar nuna adawa da matakin gwamnatin.

Sai dai duk da haka wakilin BBC a Legas Umar Shehu 'Yan Leman, ya ce jama'a sun ci gaba da taruwa domin gudanar da zanga-zanga, kuma sun sha alwashin kaiwa ga dandalin na Gani Fawehinmi.

Amma birnin ya ci gaba da kasancewa a dade - inda shaguna da bankuna da kasuwanni da ma'aikatun gwamnati suka kasance a rufe.

Rahotanni sun kuma ce jami'an tsaro sun kai samame ofishin gidan talabijin na CNN a Legas, inda suka bayar da lambar waya sannan suka bukaci da a kira su.

A Kaduna ma rahotanni sun ce daruruwan mutane ne suka fita kan tituna domin bayyana adawarsu da shirin gwamnatin kasar.

Ranar 9 ga watan Janairu ne aka fara yajin aiki da zanga-zangar wanda ya tsayar da al'amura cik a kasar mai jama'a miliyan 160, bayan da shugaban kasar ya bayyana matakin gwamnati na janye tallafin mai abinda ya sa farashin man da na sauran kayayyaki ya tashi matuka gaya.

Karin bayani