Kotu ta gayyaci Fira ministan Pakistan

Fira ministan Pakistan Yusuf Raza Gilani Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnatin Mista Gilani na tangal-tangal sakamakon matsalolin da take fuskanta

Kotun kolin Pakistan ta ce lalle Fira misnistan kasar, Yusuf Raza Gilani ya bayyana a gabanta a bisa zargin raina umarnin kotu.

Ana tuhumar sa ne da yunkurin yin rufa-rufa akan zargin cin hanci da rashawa da ake yiwa Shugaban kasar da wasu daruruwan 'yan siyasa a kasar.

Kotun kolin kasar ta ce Fira ministan kasar ya gurfana a gabanta ranar Alhamis.

Matakin da kotun ta dauka ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da zaman dar-dar tsakanin gwamnatin Mista Gilani da kuma manyan alkalan kasar.

Kotun ta fitar da sanarwar raina kotun ne bayan da antoni janar din kasar ya ce, bai samu martani daga gwamnati ba kan sake tado da batun zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa shugaban kasar Asif Zardari.

Na samun kariya daga tuhuma

Masana shari'a sun ce Mr Gilani zai ci gaba da rike mukaminsa na Fira Minista har sai an tabbatar masa da hukuncin raina umarnin kotun.

Sanarwar raina umarnin kotun na zuwa ne a lokacin da ake sauraron wata shari'a da ke bukatar gwamnatin Mr Gilani ta sake bude zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa shugaba Zardari.

Gwamnati ta dage cewa, ba za ta sake tado da zarge-zargen cin hancin ba, domin shugaban kasar na samun kariya daga tuhuma.

Masu nazari kan al'amura na cewa kwanaki masu zuwa za su tabbatar da ko gwamnatin Yusuf Reza Gilani za ta iya kammala wa'adinta na mulki.

A lokuta da dama a makon da ya gabata, alamu sun nuna cewa ba za ta iya kammala wa'adinta ba - an samu matsin lamba daga sojoji, wadanda suka yi ta cacar baki da Pira Minista.

Karin bayani