Sudan ta kwace man fetur din Sudan ta Kudu

Sudan ta kwace man fetur din Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dade ana sa'insa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

Gwamnatin kasar Sudan ta tabbatar da kwace wani daga cikin man fetur din da Sudan da Kudu ke fitarwa ta tashar ruwanta.

Gwamnatin arewacin ta ce Sudan ta Kudu bata biya wani abu daga cikin dala biliyan shida na kudaden da take binta ba, na amfani da bututunta wajen tura mai kasuwannin duniya.

Wakilin BBC ya ce Sudan ta Arewa na san Sudan ta Kudu ta biya dala talatin da shida kan tura kowacce gangar mai daya, yayin da ita kuma Sudan ta Kudu ke ganin kimanin dala daya ya kamata ta biya.

Wannan dai na daga cikin batutuwan da duka bangarorin biyu za su tattauna a wajen taron shiga tsakanin da kungiyar Tarayyar Afirka ta shirya yi a Habasha ranar Talata.

An dade ana sa'insa tsakanin Sudan da kuma Sudan ta Kudu tun bayan da Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai a bara.

Kafin samun 'yancin kan na Sudan ta Kudu dai, an shafe shekaru da dama ana yakin basasa tsakanin bangarorin biyu.

Karin bayani