Abu Qatada ya yi nasara kan Burtaniya a kotu

Abu Qatada
Image caption Burtaniya na da damar daukaka kara cikin watanni uku

Kotun kare hakkin bil’adama ta Turai ta hana Burtaniya mika malamin addinin Musuluncin nan Abua Qatada zuwa kasar Jordan domin ya fuskanci shari’a.

Alkalan sun amince da yarjejeniyar da Burtaniya ta cimma da Jordan ta kare malamin daga duk wani cin zarafi.

Amma kotun ta ce ba zai fuskanci shari’a kan ta’addanci ba kan shaidun da aka samu na ciwa wasu zarafi.

Sakatariyar cikin gida ta Burtaniya Theresa May ta ce hukuncin alkalan Turan bas hi ne “a karshe ba”

Gwamnatin Burtaniya za ta iya daukaka kara kafin hukuncin ya fara aiki nan da watanni uku masu zuwa. Idan bata daukaka ba, to dole ne a salami malamin daga tsarewar da ake yi masa.

Abu Qatada, wanda cikakken sunansa shi ne Umar Toman, yana daya daga cikin malaman addinin Musulunci masu karfin fada aji a Turai, da ke goyon bayan jihadi.

Alkalai a Burtaniya sun bayyana shi da cewa yana da illa sosai.

Bai taba fuskantar shari’a a Burtaniya ba, amma an tsare shi ba tare da an tuhume shi ba sannan ana lura da zirga-zirgarsa.

Malamin mai shaidar kasancewa dan kasar Palasdinu da kuma Jordan, an same da laifi a bayan idonsa da hannu a shirya wasu hare-haren ta’addanci a Jordan.

Sai dai y ace an samu wadancan shaidun net a hanyar cin zarafin wadanda suke kare shi kuma zai ci gaba da fuskantar hakan idan aka mayar da shi.

A shekarar 1993 ne ya fice zuwa Burtaniya bayan da aka ci zarafinsa har sau biyu.

Karin bayani