'Yan sanda na shan suka kan kubucewar dan Boko Haram

Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jagoran kungiyar Boko Haram, Imam Abubakar Shekau

Rundunar ’yan sandan Najeriya na ci gaba da shan suka bayan ta tabbatar da cewa wani mutumin nan da ta kama wanda ake zargin dan Kungiyar Boko Haram ne ya tsere.

Sukan ya biyo bayan tabbacin da sandan suka bayar na cewa mutumin da ta ce ta kama wanda ake zargin dan Kungiyar Boko Haram ne ya tsere a garin Abaji mai nisan kimanin kilomita 100 daga Abuja.

Ministan kula da harkokin 'yan sandan Najeriya Captain Caleb Olubolade ya ce an umarci sifeto Janar din 'yan sandan Najeriya Hafiz Ringim ya yi wa gwamnati bayani cikin sa'oi ashirin da hudu, yadda aka yi mutumin ya tsere daga hannun jami'ansa.

"Na bada umarnin a ci gaba da tsare dukkan jami'an tsaron da ke da alaka da tserewar mutumin". In ji Olubolade.

Ana dai ci gaba da zaman dar dar a garin na Abaji.

A yanzu haka jami'an tsaro na sintiri da motoci masu sulke a garin na Abaji, inda a wasu wuraren jama'a basu fita daga gidajensu.

Bin diddigi

’Yan sandan dai suna zargin mutumin ne mai suna Kabiru Sakkwato da hannu a harin bom din da aka kai ranar Kirsimeti a majami’ar St Theresa da ke garin Madallah, a karamar hukumar Suleja ta jihar Neja, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane arba’in.

Rahotanni sun nuna cewa an kama mutumin ne a gidan gwamnatin jihar Borno dake Abuja.

Jami'an tsaron Najeriya, sun ce da ma sun dade suna bin diddigin mutumin, kafin a kai samamen hadin gwiwar da ya kai ga kama shi.

Rundunar ta kuma ce tuni ta dakatar da kwamishinan 'yan sandan da aka dorawa alhakin tsare shi, kuma idan bincike ya nuna cewa shi da yaransa sun aikata laifi to za a gurafanar da su a gaban kotu.

Kamu da kuma tserewar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaron Najeriya ke ci gaba da shan suka saboda gazawarsu wajen shawo kan matsalar tsaro da ta addabi kasar, musamman hare-haren da ake zargin 'yan kungiyar ta Boko Haram da kaiwa.

A wata sanarwa mai dauke da sa-hannun kakakin hedkwatar ’yan sandan ta kasa, Olusola Amore, rundunar ta ce an danka mutumin ne ga wani kwamishinan ’yan sandan don ya ci gaba da gudanar da bincike.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cocin da aka kaiwa hari ranar Kirsimeti a garin Madalla

A yayin gudanar da binciken ne, in ji Mista Amore, kwamishinan ya mika mutumin ga wasu yaransa wadanda ya baiwa umurnin kai wanda ake zargin garin Abaji na Yankin Babban Birnin Tarraya, inda wasu ’ya’yan kungiyar ta Boko Haram suka yi dirar mikiya akanayarin ’yan sandan suka kuma kubutar da mutumin.

A wani bangare kuma, wata kotu babbar kotun tarayya dake Abuja ta bada belin wasu mutane 6 da ake zargin cewa 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne.

Ana tuhumarsu da tada wani bom a ofishin hukumar zabe dake garin Suleja na jihar Niger, a ranar 8 ga watan Afrilun shekarar data gabata.

Ana kuma zarginsu da jefa bomb a wani wurin gangamin siyasa a garin Sulejan, a ranar 3 ga watan Maris da ya gabata.

Za a ci gaba da sauraron karar a ranar 7 ga watan Fabrairu mai zuwa.

A Maiduguri kuma rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta ce ta ta kama wasu manyan jami'an Boko Haram, bayan wani harin da suka kai, inda sojoji biyu suka hallaka.

Karin bayani