Tattalin arzikin China ya na fuskantar koma baya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Aikin gine-gine a China

Tattalin arzikin China ya bunkasa da kashi tara da digo biyu a bara.

Hakan kuma na nuna cewa bunkasar ba ta kai ta shekarar 2010 ba.

A watanni ukun karshen shekarar ta 2011 ne dai bunkasar ta ja kafa fiye da ko wanne lokaci a shekaru biyu da rabi.

Wanann dai ya biyo fitar da kayyayaki zuwa waje da ta fuskanci tsaiko sakamakon matsalar tattalin arzikin da ke addabar Turai da Amurka.

Yayin da yanayin tattalin arziki ke kara duhu, musamman ma a Turai, manyan jami'an China sun yi gargadin cewa a 'yan watanni masu zuwa bunkasar tattalin arzikin za ta kara fuskantar koma-baya.