Hillary Clinton na ziyara a Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hillary Clinton, a lokacin da ta isa Ivory Coast

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, ta isa Ivory Coast, inda ake sa ran za ta gana da Shugaba Alassane Ouattara.

Wannan ce dai ziyara irinta ta farko da wani sakataren harkokin wajen Amurka ya kai kasar ta Ivory Coast tun shekarar 1986.

Mista Ouattara na da alaka ta kut-da-kut da Amurka, kasar da ya yi karatunsa na jami'a daga bisani kuma yai aiki da Asusun ba da Lamuni na Duniya.

A hukumance dai manufar ziyarar ita ce karfafa shirin hadin kan kasa da yafewa juna, amma akwai yiwuwar za a tattauna wasu batutuwan, wadanda suka hada da ta'addanci da fataucin miyagun kwayoyi da kuma fashi a teku.

Amurka dai ta nuna goyon baya sosai ga shugaban Ouattara a lokacin da tsahon shugaban kasa, Laurent Gbagbo ya ki ya amince da kaye a zaben da aka gudanar a yayinda kuma yasa aka yiwa Otel din da Ouattara ya ke kawanya na tsawon watanni biyar.

Dangantaka

Tun da dai aka tsare Mista Gbagbo a watan Afrailun bara, an samu zaman lafiya a kasar, kuma tattalin arzikin kasar na bunkassa da kashi tara.

Amurka dai na ba Ivory Coast fifiko a kasuwancin da take yi da wasu kasashen Afrika, sannan kuma ta taimakawa kasar da gine ginen abubuwan more rayuwa.

Kasar Ivory Coast na da tasiri sosai a siyasar yammacin Afrika, yankin da Amurka kuma ke nuna damuwa akai saboda yadda ta'adanci ke kara yaduwa da safarar miyagun kwayoyi da kuma fashin teku.

Daga Ivory Coast dai Mises Clinton za ta garzaya Togo, sannan tammala ziyarar ta a tsibirin Cape Verde.