EFCC na bincike kan biyan tallafin man fetur

Shugaban riko na EFCC Ibrahim Lamurde Hakkin mallakar hoto google
Image caption Shugaban riko na hukumar EFCC Ibrahim Lamurde

Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya EFCC,ta kai samame ofishin hukumar kula da kayyade farashin man fetur.

Hukumar EFCC ta ce ta kwace wasu takardu a wani bangare na binciken da ta kaddamar kan zargin cin hanci da rashawa a harkar shigo da man fetur da kuma biyan kudaden tallafi a kasar.

Matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da jama'a ke komawa aiki bayan da aka rage farashin man fetur sakamakon yajin aikin da aka shafe mako guda ana yi.

Najeriya ce kan gaba wajen fitar da danyan mai a nahiyar Afrika, amma tana shigo da tataccen mai ne zuwa kasar tata.

Yajin aikin wanda aka shafe kwanaki shida ana yi, an kira shi ne bayan da shugaba Goodluck Jonathan ya janye tallafin mai a ranar 1 ga watan Janairu, wanda gwamnati ta ce yana lashe dala biliyan 8 a duk shekara.

Ta ce za a kashe kudaden ne wajen ayyukan gina kasa sannan ta ce wasu 'yan tsiraru ne kawai ke amfana da kudaden tallafin.

Har da kamfanin NNPC

Mai magana da yawun hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya shaida wa BBC cewa sun kai samame ofisoshin hukumar kayyade farashin mai ta PPPRA a Legas da kuma Abuja.

Rahotanni a kafafen yada labarai na Najeriyar sun ce bincike zai hada da babban kamfanin mai na kasa NNPC.

A ranar Litinin ne gwamnati ta bayar da sanarwar rage farshin man zuwa naira 97 a kan lita, bayan da ta dawo da wani bangare na tallafin.

Farashin man ya tashi daga naira 65 zuwa 145 lokacin da aka cire tallafin.

Man fetur ne ke samar da kashi 80 cikin dari na kudaden shiga ga kasar, amma cin hanci da rashawa da almubazzaranci ya hana ta samun ingantattun matatun mai domin tace man a cikin gida.

Tallafin mai ya sanya man ya fi arha a makwaftan kasashe, abinda ya sa ake fasakwaurinsa zuwa kasashen waje domin samun karin kudade.

Karin bayani