Ana zargin kyaftin din jirgin Italiya da sakaci

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jirgin ruwan Shakatawan Italiya da ya kife

Jami'an tsaron gabar tekun Italiya sun ce har yanzu da sauran fatan gano mutane ashirin da taran da suka bace bayan da wani jirgin ruwan shakatawa ya kife daura da gabar.

An tabbatar da cewa mutane shida sun mutu.

Kamfanin dillancin labarai na Italiya (Ansa) ya ba da rahoton cewa hukumomin da ke kula da gabar ruwan na zargin kyaftin din jirgin, Francesco Schettino, da yin sakaci.

Wani mai shigar da kara , Francesco Verusio, ya ce kyaftin din na cikin tsaka mai wuya saboda ya bar jirgin alhalin akwai fasinjoji da dama a ciki wadanda ya kamata a fara tserar da su tukuna.

Kamfanin da ya mallaki jirgin ya kuma zargi kyaftin din da kauce hanya da gangan, sai dai kuma kyaftin ya nace cewa bai saba ka'ida ba.

Sakaci

Akwai dai hasashen da jama'a da dama ke yi kan dalilan da su ka haddasa hatsarin jirgin ruwan, amma a yanzu haka za'a iya tantance taka mai mai abun da ya faru bayan an gano daya daga cikin na'urar nadan bayanai a jirgin.

Kamfanin dillancin Labarai na Italiya, (Ansa) ya ruwaito cewa, daya daga cikin na'urar da aka gano na dauke ne da wata hira da kyaftin din Jirgin yayi da wani jami'in hukumar kula da jiragen ruwa a gabar teku su ka a lokacin da jirgin ke kifewa.

Jami'in dai a hirar ya bukaci kyaftin din jirgin da ya tsara yadda za'a kwashe mutanen jirgin a yayinda yake kan nitsewa.

Jami'in ya kuma nemi kyaftin din da ya gaya masa yawan mata da yara dake jirgin amma sai ya ki.

Amma a yayinda aka samun karin bayanai kan abubuwan da suka haddasa hatsarin jirgin, akwai alamar tambaya kan kyaftin da cewa ya yi sakaci.

Karin bayani