Rasha ta yi gargadi kan kaiwa Iran hari

Rasha ta yi gargadi kan kaiwa Iran hari Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ministan harkokin wajen Iran Akbar Salehi lokacin ziyar da ya kai Turkiyya

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce daukar wani matakin soji daga kasashen Yamma kan Iran, zai zama wata "babbar masifa" a duniya.

Mista Lavrov ya kuma ya nuna rashin goyan bayansa ga kakabawa Tehran karin takunkumi.

Ya ce daukar matakin zai haifar da mummunan sakamako ta hanyar samun dubban 'yan gudun hijira daga Iran, kuma zai haifar da zaman dar-dar ta fuskar addini a yankin.

Tunda farko ministan tsaron Isra'ila Ehud Barak ya ce "ba a tsaida matsaya" kan matakin kaiwa kasar ta Iran hari ba.

A gefe guda kuma Ministan harkokin wajen Iran ya ce mai yiwuwa a sake komawa fagen tattaunawa kan shirin nukiliyar kasar a birnin Santanbul na kasar Turkiyya.

Ali Akbar Salehi ya shaida wa manema labarai a wata ziyara da ya kai Turkiyya cewa tattaunawa ta yi nisa wurin neman wuri da kuma sanya ranar da za a fara tattaunawar.

Sai dai ma'aikatar kula da harkokin wajen Burtaniya ta ce "babu wata tattaunawa ko wani cikakken shirin yin haka", domin Iran ba ta nuna wata alamar cewa a shirye take ta bayar da amsar wasikar da tarayyar Turai ta aika mata ba, domin tattaunawa ba tare da wani sharadi ba.

"Idan dai har bata yi hakan ba, to kasashen duniya za su kara matsa lamba a kanta ta hanyar kakaba mata takunkumi ta hanyoyin da suka dace".

Sai dai mista Sergei Lavrov ya ce matakan karfafa takunkumin kasashen yammaci kan shirin makamashin nukiliyar Iran na duba yadda za a gurgunta tattalin arzikinta da kuma haddasa rashin jituwa a cikin Iran din.

Karin bayani