Obama ya yi fatali da shawarar shimfida batutan mai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Barak Obama na Amurka

Shugaba Obama ya yi fatali da shawarar wani kamfanin Canda ta shimfida maka-makan bututan mai daga kasar ta Canada zuwa Jihar Texas.

Mista Obama ya zargi abokan adawarsa na jam'iyyar Republican da ke majalisar dokoki da yanke shawara ba tare da baiwa gwamnati isasshen lokaci don ta gudanar da bincike a kan illar aikin ba.

Ministan albarkatun kasa na Canada, Joe Oliver, ya ce ya yi amanna shimfida bututan wadanda ake kira Keystone XL pipeline, zai amfani kasashen biyu.

"Wannan aiki zai samar da dubun dubatar ayyukan yi a Amurka da ma Canada; zai kuma taimaka wajen wadata Amurka da makamashi." In ji Joe Oliver

Kamfanin dai na da damar sake neman izini idan ya yi kwaskwarima ga tsare-tsarensa.

Siyasa

Batun bututun man dai ya zama wani babban al'amari siyasa kasar.

Masu fafutukar kare muhalli dai sunyi gargadin cewa idan har aka amince da shirin, zai gurbata ruwan shan al'ummar Nebraska.

Tun a shekarar 2008 ne kasar Amurka tace tana nazari gama da shimfida batutun man, amma a bara ne dai 'yan jami'iyyar adawa ta Republicans su ka baiwa gwamnati Obama wa'adin kawanaki shida domin ta yanke shawara game da shirin.

'Yan jam'iyyar Republican da dama dai na ganin aikin zai samar da ayyukan yi ga daruruwan 'yan Amurka.

Pira Ministan Canada Stephen Harper ya shaidawa Shugaba Obama, rashin jin dadinsa kan yadda Amurka ta sa kafa ta shure shirin, amma ya ce yana fatan Amurka za ta sauya matsayarta a kan batun.