Fira Ministan Pakistan ya kare kansa a gaban kotun koli

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Pira Ministan Pakistan, Yusuf Raza Gilani

Priyi ministan Pakistan Yusuf Raza Gilani, ya bayyana a gaban kotun kolin kasar, domin bayar da bahasi akan dalilan da suka sa, ya ki daukar matakai akan zargin cin hancin da rashawar da ake yiwa Shugaba Zardari.

Tare da ayarin ministocinsa da kuma lauyoyin da ke kare shi, Mr Gilani ya bayyana cewar shugaban kasar yana da kariya ce da ta hana hukunta shi a lokacin da ya ke kan karagar mulki.

Yace: "mu mutane masu girmama da mutunta Kotu ne, kuma masu tsayawa ne daram akan irin shawrwarin da muka dauka. To amma kuma akwai tsarin mulki a tsakaninmu. Shawarar da aka bani kuma abun da na yi imanin da shi shi ne, shugaban kasa yana da rigar kariyar akan gurfanar da shi a gaban kotu, ko a ciki ko kuma a wajen kasa."

An dage ci gaba da sauraron bahasi a tuhumar Mista Gilani da raina umurnin kotun zuwa ranar uku ga watan Fabrairu.

Pakistan din dai na fama ne da takaddamar siyasar da ke barazanar kawo karshen gwamnatin Mista Gilani.

Bayyanar Pira Ministan Pakistan Yusuf Razaka Gilani a gaban kotun kolin kasar, wata takkadama ce ta baya baya nan ta siyasa da ta kunno kai, wadda ta hada da gwamnatin kasar da bangaren shari'a da kuma Sojojin kasar.

Shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zadari na cikin 'yan siyasar kasar da hukumomi a Switzerland ke tuhumar su da cin hanci.

Karin bayani